Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya bayyana cewa: Iran ta ƙuduri aniyar karya killacewar da aka yi mata kuma za ta mayar da martani da cikakken ƙarfi ga duk wani sabon hari
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Reza’i, ya bayyana cewa: Shirin Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da tawagarsa da suka sha kaye na sanya wa Iran matakan killacewa, ba wani abu ne mai ban mamaki, kuma ba zai yi nasara ba kamar yadda dabarun yaƙi suka gaza.
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin “X”, Manjo Janar Reza’i ya ƙara da cewa: Mutanen Iran da sojojin ƙasa da dukkan cibiyoyin gwamnati sun ƙuduri aniyar karya wannan killacewa tare da mayar da martani da cikakken ƙarfi ga duk wani sabon hari.