Araqchi: Neman Rusa Hukumar Haramta Makamai Masu Guda Kuskure Ne

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Hana ayyukan Ƙungiyar Haramta Makamai Masu Guba da Amurka ta yi babban abin kunya ne Ministan Harkokin Wajen

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Hana ayyukan Ƙungiyar Haramta Makamai Masu Guba da Amurka ta yi babban abin kunya ne

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya yi ikirarin cewa: Amurka na jefa zaman lafiya da tsaron duniya cikin haɗari da gangan ta hanyar toshe ayyukan Kungiyar Haramta Makamai Masu Guba (OPCW), yana mai bayyana wannan matakin a matsayin abin babban abin kunya.

A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X, Araqchi ya rubuta cewa: “Amurka tana da matukar damuwa game da makamai masu guba har ta kusan gurgunta masu sa ido kan wadannan makamai!”

Ministan Harkokin Wajen Iran ya kara da cewa, yana gargadin illar wannan matakin, cewa za a iya tilasta wa OPCW ta dakatar da ayyukanta da kuma rage manyan shirye-shiryenta.

Araqchi ya jaddada cewa ta hanyar toshe ayyukan kungiyar, Amurka na barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya da gangan, yana mai jaddada cewa wannan dabi’a abin kunya ne.

Yemen

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted