Rasha Za Ta Kara Yawan Alkamar Da Take Kai Wa Kasashen Afirka

Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin

Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin da take fitarwa zuwa wasu kasashen Afirka da kaso 19% da kudin da su ka hau da dala biliyan 7.

Wasu kasashen da Rashan za ta linka yawan alkamar da take aikewa su ne Moroko, Najeriya da kuma Kamaru.

Yawan alkamar da kasar Rashan za ta aike zuwa Moroko ta kai ton 124,000,a 2024 kuwa yawan alkamar da ta aikewa ita ton 54,000.

Ita kuwa kasar Najeriya yawan alkamar da Rashan ta aike mata ta tashi daga ton 48,000 zuwa ton 131,400.

Alama ce muhimmin kayan abincin da kasar Rasha take aike wa nahiyar Afirka. A shekarar 2024 da ta gabata ta kai wa nahiyar alkama da kudinta su ka kai dala biliyan 7.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments