Rahotanni sun bayanna cewa kakakin fadar kremlin Dimitry peskov yayi gargadi game da barazanar baya yana nan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubios yayi da cewa akwai yiyuwa Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya.
Ci gaba da gwajin nukiliya ga Amurka zai kara fadada zaman dardar a duniya, kuma zai kawo cikasa ga kokarin shawo kan yaduwar makamai na tsawon shekaru da ake yi, sannan ya sake farfado da fargabar sake shiga sabuwa gasar makamai a dangantakar Amurka da rasha da ta riga ta tabarbare
Idan ana iya tunawa a ranar 29 ga watan oktoba ne shugaban Amurka Donald trump ya umarci maaikatar tsaron Amuka da ta ci gaba da gwajin nukiliya wanda yake nuna yiyuwar samun sauyi a manufofin Amurka.
A ranar 5 ga watan nuwamba shugaban kasar rasha viladimir putin ya umarci ministocinsa da su fara shirin uiyuwar dawo da gwajin nukiliya dominmayar da martani ga shirin Amurka