Mataimakin shugaban kasar Rasha Nikolai Patrushev ya bayyana cewa; duk wani hari da za a kai wa yankin Kalligrad to zai fuskanci mayar da martani mai tsananin gaske.
Mataimakin shugaban kasar ta Rasha ya kuma ce; A bisa akidar tsaro ta Rasha duk wani hari da za a kai mata, to zai sa kasar ta yi amfani da dukkanin makaman da take da su, domin mayar da martani akan abokan gaba, daga ciki har da makaman Nukiliya idan bukatar haka ta taso.
Nikolai Patrushev wanda kamfanin dillancin labarun Sputnik ya yi hira a shi, ya ce;yankin Kallingrad kasar Rasha ne, don haka duk wani hari da za a kai masa zai sa su yi amfani da dukkanin karfin da suke da shi, wajen mayar da martani, har da makaman Nukiliya.
Mataimakin shugaban kasar ta Rasha ta kuma ce; Rasha tana sane da Shirin da kasashen yammacin turai su ke da shi, irin wannan, don haka Rasha tana da makaman da take da bukatuwa da su, domin kare yankin na killingirad.
Nikolai Patrushev ya bayyana shugabanin kasashen yammacin na yanzu da cewa, daidai suke da ‘yan Nazi,don haka za su shiga kwandon sharar tarihi kamar yadda magabatansu ‘yan Nazi na baya su ka shiga.
A baya kadan ne dai kwamandan sojan Amurka a turai da Afirak janar Chiristopher Donaho ya bayyana cewa; Nato ta shirya yadda za ta raunana layin tsaron da Rasha take da shi a yankin Kallingrad, domin karfafa hanyoyin aiki tare a tsakanin kasashen Nato.
Shi kuwa mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Rasha Dmity Viskov, ya ce; Fadar gwamnatin kasar tana daukar wannan barazanar da hatsari.