Rasha ta mayar wa da Trump martani kan yakin Ukraine

Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine. Mai magana da yawun

Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine.

Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ce Rasha na nan a kan matsayinta na zakanyar kasa, kuma tana cikin kwanciyar hankali ta fannin tattalin arziki.

Peskov ya tabbatar wa manema labarai cewa babban kuskure ne a yadda ake cewa Ukraine za ta iya yin nasara wajen karbe ikon yankunanta da ke hannun Rasha.

Bayan ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a New York, Trump ya ce Ukraine na iya kwato dukkan yankunan da ta rasa, inda ya bayyana Rasha a matsayin kyanwar Lami.

Ya kuma ce tattalin arzikin Rasha na cikin gagarumar matsala.

Tun da farko Shugaba Trump ya bayyana Rasha a matsayin kasar da ke kallon kanta a matsayin wadda ta fi kowacce kasa karfin soji, alhali kuma abin ba haka yake ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted