Rasha Ta Kai Wa Ukiraniya Hari Mafi Muni Tun Farkon Yaki

Sojojin Rasha sun kai hare-hare mafi muni akan cibiyoyin soja da muhimman cibiyoyi a kasar Ukiraniya da su ka hada da birnin Kiev. Sojojin na

Sojojin Rasha sun kai hare-hare mafi muni akan cibiyoyin soja da muhimman cibiyoyi a kasar Ukiraniya da su ka hada da birnin Kiev.

Sojojin na Rasha sun yi amfani da kamamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake da su ka haddasa tashin gobara.

Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kharikiev ya bayyana cewa; A kalla mutane 10 su ka jikkata a bisa kididdigar farko.

 Ita kuwa rundunar sojan saman kasar ta Ukiraniya ta sanar da cewa; an yi amfani da makamai masu linzami samfurin “Cruise” wajen kai harin.

Su ma sojojin na Rasha sun sanar da cewa, sun kai wa Ukiraniya hare-hare akan sansanonin soja da kuma muhimman cibiyoyin kasar ta hanyar amfani da makamai masu linzami samfurin “Caliver” da kuma jirage marasa matuki.

A nata gefen ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 82 da Ukiraniya ta harba daga cikin har da saman birnin Moscow.

Tun a makon da ya shude ne dai shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin ya yi alkawalin mayar wa da Ukiraniya martani saboda hare-haren da ta kai wa wasu filayen saukar jiragen sama na soja da su ka hada wadanda suek dauke da muhimmanci jiragen yakin da Rashan take takama da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments