Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki wajen kai hare-hare a kan birnin Kiev da kuma wasu gundumomi 9 na kasar.
Rundunar sojan saman kasar Ukiraniya ta ce; Kasar tasu ta fuskanci munanan hare-hare da makamai masu linzami a cikin gundumomin gabashi, yammaci da kuma babban birnin kasar Kiev.
Rundunar soja da take tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kiev ta sanar da cewa; Daga cikin wuraren da aka kai wa hare-haren da akwai tashar jirgin kasa, hakan nan kuma muhimman cibiyoyi da gidajen fararen hula.
Magajin birnin Vitali Klitschko ya sanar da cewa; Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu mutane 20 su ka jikkata sanadiyyar harin na Rasha. Haka nan kuma gobara ta tashi lokacin da makamai masu linzami da jirage marasa matuki su ka fada a cikin unguwanni 3 na birnin.
A can kasar Rasha kuwa, an sanar da kakkabo jirage uku marasa matuki da Ukiraniya ta harba wa birnin Moscow, haka nan an dakatar da kai da komowar jirage a filiyen jiragen sama na birnin Moscow, da kuma Caloga.
Sai dai kuma wata majiyar a Rasha ta ce gobara ta tashi a cikin wani gida a garin Ingilz, saboda fadawa jirgin sama maras matuki akansa.
Yaki dai ya barke ne a tsakanin Rasha da Uniraniya tun a ranar 24 ga watan Febrairu 2022, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane 12,000 kamar yadda MDD ta ambata.