Fadar mulkin kasar Rasha Krimlne ta sanar da cewa, shugaban kasar Valdmir Putin ne ya sa ido akan yadda rundunar dake kula da makaman Nukiliya ta gudanar da rawar daji a sansnain “Blisitiks”.
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar dake kula da muhimman makakan Nukiliyar kasar ta Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami samfurori mabanbanta.
Haka nan kuma fadar gwamnatin Rashan ta ce, an gudanar da dukkanin gwaje-gwajen cikin nasara, an kuma yi ne domin tabbatar da cewa rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana.
A wani labari mai alaka da Rasha, ma’aikatar harkokin waje ta gargadi kasashen turai akan kokarin bai wa Ukiraniya kudadenta da suke a cikin bankunansu.
MA’aikatar harkokin wajen Rasha ya fadawa kasashen turai din cewa martanin da kasar za ta mayar idan har su ka kuskura su ka taba mata kudinta dake cikin bankunansu, zai zama mai tsanani.
Kasashen turai dai suna tattauna hanyoyin doka da za su basu damar dibar kudaden Rasha da suke cikin bankunansu, domin bai wa kasar Ukiraniya ta sayi makamai da su.