Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington.
“Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin.
Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole.
Vladimir Putin ya dage kan cewa tattaunawar da Rasha da Amurka suka yi a makon jiya a Saudiyya, wadda ita ce ta farko a wannan matakin tun farkon rikicin, na da nufin karfafa kwarin guiwa tsakanin Moscow da Washington.
Kafin hakan dai Ministocin harkokin wajen Rasha da Amurka Sergei Lavrov da Marco Rubio sun tattauna a Saudiyya kan “matsalolin da ke da nasaba da rikicin na Ukraine, amma ba batun rikicin Ukraine din ba,” a cewar Vladimir Putin.