Jakadan kasar Rasha a Tehran ya bayyana cewa kasashen yamma ba a shirye suke su bude tattaunawa ta gaskiya da kasar Iran a kan shirinta na makamashin nukliya ba.
Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Alexey Yurievich Dedov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha.
Ya kuma kara da cewa, sakamakon taron gwamnonin hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA a ranar 5 ga watan Yunin da ya gabata ya tabbatar da hakan.
Dedov, ya kara da cewa duk tare da hadin kan da gwamnatin JMI take bayarwa ga hukumar ta IAEA amma gwamnonin hukumar sun kada kuri’an rashin amincewa da Tehran, inda suke zargeta da boye wasu al-amura masu muhimmanci ga hukumar ta IAEA a cikin shirin ta na makamashin nukliya.
A taron ranar 5 ga watan Yunin day a gabata dai, cikin gwamnoni 35 a hukumar, 20 daga cikinsu sun tabbatar da zargin da akewa Tehran, 2 suka ki amincewa a yayinda 12 suka ki kada kuri’unsu.
Iran dai ta yi tir da hukumar, ta kuma kara da cewa matsayin da ta dauka ba zai taba sa kasar Iran ta jada baya a kan hakkinta na amfani da fasahar nukliya ta zaman lafiya ba.