Rasamani: Asarar Yakin HKI Ta Kai Dalar Amurka Biliyan 14

Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar

Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar Amurka biliyan 14, tare da bayyana cewa kasar Rasha ta bijiro da cewa za ta taimaka.

Rasamani ya fada wa Radiyon “Sputnik” na Rasha cewa; Suna ci gaba da aiki tare da babban bankin duniya, domin tantance barnar da yakin Isra’ila ya haddasa a Lebanon.”

Bugu da kari ministan ayyukan na kasar Lebanon ya kuma ce; Ma’aikatar ta fara aikin debe baraguzai a cikin garuurwan da za su iya isa, wadanda babu sojojin HKI a cikinsu.”

Haka nan kuma ya ce; Kasar ta Lebanon da kuma Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni suna aiki domin fito da tsarin aiki na sake gina wuraren da yakin ya rusa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments