Ranar Quds : Hamas ta bukaci masu huduba su sadaukar da jawabansu kan Falastinu

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya.

Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa.

A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya.

“Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na duniya da su fito a ranar Juma’a, Asabar, da Lahadi mai zuwa don kare Gaza, Quds, da masallacin Aqsa, da goyon bayan juriyar jama’armu, da yin tir da laifuffuka da tsare-tsare na gwamnatin mulkin mallaka a kan kasarmu, mutanenmu, da wurarenmu masu tsarki da ake yi a Gaza.” Inji Hamas

Hamas ta kuma yi kira da a ci gaba da matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila don kawo karshen zalunci da kisan kiyashi ga Palasdinawa, Har ila yau sanarwar ta yi kira ga masu hudubar sallar Juma’a da su sadaukar da jawabansu na wannan Juma’a kan batun Falastinu, domin kwadaitar da al’ummar musulmi wajen karfafa goyon bayansu ga al’ummar Palastinu da suke fafutukar kare kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments