Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita.
Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar a baya. Duk da haka, Pretoria ta dage cewa shugabancin da ake yi nak aba-karba an mika shi ga wani jami’in Amurka.
Bayan kauracewa taron shugabannin G20 da aka gudanar a Johannesburg a ranar 22-23 ga Nuwamba a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu, Trump ya maimaita ikirarinsa na cewa gwamnatin kasar mai rinjayen bakaken fata tana nuna wariya ga tsirarun fararen fata.
A jawabinsa, Ramaphosa ya kira zarge-zargen Trump na kisan kare dangi da kwace filaye daga fararen fata da cewa ba gaskiya ba ne, zargui ne maras hujja balantana makama, yana mai sake jaddada cewa “Afirka ta Kudu cikakkiyar memba ce da aka kafa G20 tare da ita.”
Rikicin da ke tsakanin Washington da Pretoria ya fara kamari ne a farkon 2025. A ranar 14 ga Maris, Amurka ta kori jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, bayan ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da abokansa da haɓaka ajandar duniya ta masu ra’ayin wariyar launin fata