Shugaban kasar Iran Hujatul-Islam Ibrahim Ra’isi wanda ya gabatar da jawabi a wurin girmama masu karatun kur’ani da yi masa hidima karo na ashirin da tara, ya ce; A yayin baje kolin alkur’ani mai girma na bana, an gabatar da wasu sabbin hanyoyi na koyar da littafin Allah, don ya haka ya zama wajibi a girmama masu yin wannan hidimar.
Sayyid Ibrahim Ra’isi ya kuma ce; Babu wani abu da zai bai wa jinsin bil’adama sa’ada a doron kasa idan ba riko da koyarwar alkur’ani mai girma ba, domin shi cikakken littafi ne dake dora mutum akan hanyar shiriya.
Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Rayuwar da aka gina ta akan koyarwar alkur’ani tana da saukin tafiyarwa.
Shugaba Ra’isi ya ziyarci wajen baje kolin al’kurni mai girma na shekara-shekara da aka bude a nan Tehran, wanda na bana shi ne karo na 31.