Rahoto : Sama da mutum miliyan 80 aka raba da muhallansu a fadin duniya

Sabbin alkaluma da cibiyar sanya ido kan yadda ake raba mutane da muhallansu da kuma hukumar kula da yan gudun hijira ta Norweian Refugee Council

Sabbin alkaluma da cibiyar sanya ido kan yadda ake raba mutane da muhallansu da kuma hukumar kula da yan gudun hijira ta Norweian Refugee Council suka fitar sun bayyana cewa yanzu haka akwai sama da mutum miliyan 80 da aka raba da muhallansu a fadin duniya, kuma wannan ne mafi yawa da aka taba samu a tarihi.

Alkaluman da cibiyar sun nuna cewa yawan mutanen ya nunka fiye da sau biyu a cikin shekaru shida.

Rahoton ya ce kimanin mutum miliyan 74 ne rikice-rikice suka tursasa wa barin gidajensu.

Yakin Sudan kawai ya tarwatsa mutum sama da miliyan 11 – wanda shi ne mafi yawa da aka samu a kasa daya.

Sai kuma bala’o’in da sauyin yanayi ke haifarwa wadanda suka yi sanadin korar kimanin mutum miliyan 45 daga gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments