Rahoto : Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Tsakiyar Turai

Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden

Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana.

A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine.

A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland.

Shugaba Donald Trump yana kokarin kawo karshen yakin Ukraine da aka shafe fiye da shekaru uku anayi tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cimma nasarar warware matsalar ba.

Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta dauki karin nauyi wajen kare kanta ta hanyar kara kashe kudi kan harkokin tsaro, da kuma jagorantar samar da makamai ga Ukraine.

A halin yanzu, akwai kimanin sojojin Amurka 100,000 da ke Turai, inda 65,000 daga cikinsu ke zama a nahiyar ta dindindin, to saidai masana na ganin janye dakarun na Amurka zai karawa Rasha karfi ne a yakin da ta ke yi Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments