Rage tallafi na kara tsananta wahalhalun jin kai a Zirin Gaza na Falasdinu
Matsalar jin kai a yankin Gaza na ƙara ta’azzara, inda dubban mutanen da suka rasa matsugunansu ke fuskantar mawuyacin hali da kuma ƙarancin tallafin abinci da kayan masarufi.
Wannan ya zo ne bayan da Hukumar Abinci ta Duniya {WFP} ta sanar da rage tallafin abinci a yankin Gaza saboda ƙarancin kuɗaɗen tallafi, wanda ya bar dubban Falasɗinawa a yankin suna fuskantar barazanar yunwa a yayin da ake ci gaba da kai musu hare-haren wuce gona da iri daga sojojin mamayar Isra’ila.
Sanarwar ta zo ne bayan rikicin jin kai da ke ci gaba da faruwa da kuma raguwar ƙarfin jama’a na biyan buƙatunsu na asali, shekaru uku bayan fara kai hare-hare wuce gona da iri daga gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila kan yankin da kuma barna suke aiwatarwa na rushe-rushen gine-gine da korar Falasdinawa daga matsugunsu gami da wahalhalun rayuwa da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a dukkan bangarorin rayuwa.