Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qolibof ya bayyana cewa kungiyar BRICS wata dama ce ta kaucewa danniya da babakeren da Amurka take kudaden sauran kasashen duniya.
Qolibof yana bayyana haka ne a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Brazil Dowi Alku-Lomubre a gefen taron shuwagabannin majalisun dokokin kungiyar BRICS wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Brazia na kasar Brazil.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin Iran yana fadar cewa kasashen Iran da Brazil suna da fahinta iri guda dangane da yenci da kuma zama yentacciyar kasa. Don haka tare da wannan ana iya gina dangantaka ta bunkasar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu tare da wannan fahintar.
Qolibof ya kara da cewa abu mafi muhimmanci na tattalin arzikin wanda kasashen biyu zasu fara karfafawa sun hada da ayyukan Noma musayar kayakin kasuwanci, na shigowa da fitarwa da kuma bangaren ilmi.
Ya kuma bayyana cewa a ganawarsa da ministan harkokin noma ya bayyana cewa abu na farko wanda kasashen biyu zasu yi shi tabbatar da kwamitin tattalin arzikin kasashen biyu ya fara aiki.