Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba

Fira ministan kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahaman al thani yayi gargadi game da ci gaba da kai hare-hare da kame falasdinawa da HKi ke

Fira ministan kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahaman al thani yayi gargadi game da ci gaba da kai hare-hare da kame falasdinawa da HKi ke yi a yankin gaza, ya jaddada cewa shirin da shugaban Amurka ya bullo da shi na zaman lafiya zai zama gaskiya ne idan isra’ila ta janye dukkan sojojinta a yankunan da ta mamaye a gaza.

Da yake bayani a wajen taron da aka gudanar da birnin Doha al thani yace yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kwashe watanni biyu da cimmawa tsakanin Hamas da Isra’ila ta kai wani muhimmin matsayi adaidai lokacin da matakin farko na shirin da trump ya bullo da shi mai matakai 20 yake gaba da karewa.

Ya kara da cewa masu shiga tsakanin na kasa da kasa suna kokarin ganin an shiga mataki na biyu na yajrejeniyar zaman lafiya da aka cimma, wanda ke nufin karfafa yarjejeniyar da kuma kafa tsarin siyasa na dogon lokaci.

A banagre guda kuma ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan Fidan  yayi jawabi a wajen taron inda ya nuna damuwarsa game da shirin zaman lafiya a gaza, yana nuna rashin tabbas game da kasashen dake da hannu wajen shiga tsakani na samar da muhimman abubuwan da ake bukata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted