Qalibof: Dole Ne Musulmi Su Hada kai Don Matsin Lamba Ga HKI

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Kolibof yayi kira ga kasashen musulmi sun hada kai don sanyawa HKI biriki kan abinda take aikatawa a

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Kolibof yayi kira ga kasashen musulmi sun hada kai don sanyawa HKI biriki kan abinda take aikatawa a gaza, na kasar Falasdinu da ta mamaye, da kuma kawo karshen burin Natanyahu na samar da Isra’ila babba.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, gaza ne katangar Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta da karshe a ta’asan da ta aikata a kan musulmi.

Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya jumma’a ya kuma kara jan hankalin kasashen musulmi kan shirin Natanyahu na samar da Isra’ila babba a fili, don tabbatar da wa musulmi kan cewa, ba zasu iya fuskantar HKI ba.

Ya yi kira ga kasashen musulmi su gaggauta gamawa da HKI a falasdinu kafin lokaci ya kure.

A ranar talatan da ta gabata ce Natanyahu, ya ce yana kan aikin ubangiji na samar da Isra’ila babba.wanda ya hada da kasar Jordan da kuma masar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments