Qalibof: Dole Ne A Ladabtar Da Amurka Kan Yakin Da Iran

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa, dole ne Iran ta ladabtar da gwamnatin kasar Amurka kan laifuffukan da ta aikata

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa, dole ne Iran ta ladabtar da gwamnatin kasar Amurka kan laifuffukan da ta aikata saboda yakin da ta dorawa JMI na baya bayan nan.

Banda haka a tilasta mata amincewa da sharuddan kasar Iran na bude mashigar ruwa ta Hurmus.

Tashar talabijan ta Presstv  a nan Tehran ta nakalto Qalibaf shugaban kwamitin tattaunawa da Amurka yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa, a halin yanzu iran tana neman kawo karshen yaki da Amurka da kuma samar da yanayi wanda mutanen kasar zasu shiga harkokinsu ba tare da jin tsoron za’a sake fada masu da yaki ba.

Kakakin majalisar ya ce, Iran bata da zabi wajen yaki don kare kanta, kare mutanen kasar da kuma tabbatar da diyaucunta. Sanan a gefe guda kuma a duk lokacinda wata dama da sansantawa ta bullo, sasantawa wacce zata yi adalci ga kasar suna iya amincewa da shi.

Y ace zamu yi yaki a duk lokacinda yaki ya zama wajibi a kammu sannan mutane kuma kan teburin tattaunawaa tare da sharaddata.

Kuma nasara dai daga wajen All..ne kawai take samuwa. A kansa muka dogara kuma shi ne mabuwayi mai hikima.

Dangane da wargajewar tattalin arzikin kasar Iran wanda sakataren kudin Amurka Scott Bessent

 Ya yi hasashe kuma, qalibof yayi masa darayi saboda yanda ya sha nanata cewa zuwa rana kasa tattalin arzikin kasar Iran zata fadi. Amma lokacin ya zo ya wace ba tare da hakan ya faru ba. Y ace mai yuwa a bashi kyautar Nobel don wadannan hasashen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted