Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya mika sakon gaisuwar idin Nowruz na sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Nowruz, na shigowar bazara da kuma sabuwar shekara ta Farisa.
Putin ya kuma aike da sakon fatan alheri ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar a ranar Juma’a.
Nowruz, wanda ke nufin Sabuwar Rana, ita ce ranar farko ta watan Farvardin na kalandar Farisa. Ranar a mafi yawan lokuta tana kamawa ne a ranar 20 ga Maris amma a duk bayan shekaru tana tana kamawa daidai da 21 ga Maris.
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ranar Nowruz ta duniya a shekara ta 2010, inda ta bayyana ta a matsayin bikin bazara na kalandar Farisa, wanda aka shafe shekaru sama da 3,000 ana gudanar da ita.
Hakanan a cikin shekarar 2009, an sanya Nowruz a hukumance a cikin jerin abubuwa na tarihi da al’adu na bil adama na hukumar UNESCO.