Politico: Sojojin Ukiraniya Suna Fuskantar Matsin Lamba Da Karancin Mayaka

Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka. Wannan matsin lambar

Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka.

Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da suke guduwa daga filin yaki suna karuwa.

Jaridar ta kuma kara da cewa; Babban hafsan hafsoshin kasar ta Ukiraniya ya bayar da umarnin a dauki sojojin sama 5000 a mayar da su na kasa.

Da akwai tsoron cewa kasar ta Ukiraniya tana rashin kwararrun sojojinta, da ba za ta iya maye gurbinsu a cikin sauki ba idan har aka tura su zuwa filin daga.

A gefe daya, ministan harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa; A halin yanzu Ukiraniya tana yin asarar mutanenta ba wai kudi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments