Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya soki abunda ya danganta da barazanar Amurka ga Teheran, yana mai cewa kasarsa a shirye take ta shiga tattaunawa ta hakika ba tare da barazana ba.
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman tattaunawa ta gaskia, a yayin da suke barazana ga Iran a daya bangaren kuma suna neman yin shawarwari,” in ji Pezeshkian a ranar Asabar.
“Idan kuna neman shawarwari, to me yasa kuke yin barazana? A yau, Amurka ba wai kawai ta wulakanta Iran ba har ma da duniya, kuma wannan hali ya saba wa bukatar tattaunawa,” in ji shi.
Kalaman na Pezeshkian sun zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Tehran da ta shioga shawarwari kai tsaye kan shirinta na nukiliya yayin da ya yi barazanar jefa bama-bamai a Iran idan diflomasiyya ta gaza.
A ranar Lahadin da ta gabata, ne Trump ya sake yi wa Iran barazanar kai harin bama-bamai da kuma lafta mata takunkumai masu tsauri a karo na biyu idan ba ta cimma matsaya da Washington ba kan shirinta na nukiliya, a yayin da kuma Amurka ta kara tura karin jiragen yaki zuwa yankin.
Tunda farko Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araghchi ya sake nanata shirin Tehran na shiga shawarwarin da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, saidai yana mai gargadin cewa barazanar Amurka na dagula halin da ake ciki.