Pezeshkian ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Yahya Sinwar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshian ya mika sakon ta’aziyyar shahadar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Yahya Sinwar. “Kisan da ake yi wa shugabanni da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshian ya mika sakon ta’aziyyar shahadar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Yahya Sinwar.

“Kisan da ake yi wa shugabanni da kwamandojin gwagwarmaya   ba zai raunana juriyar da al’ummar musulmi suke yi wajen fuskantar girmakan Isra’ila ba.”  in ji shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian.

Pezeshkian ya fitar da sako a wanann Juma’a bayan da kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa Sinwar ya yi shahada a wata arangama ta kai tsaye kuma gaba da gaba da sojojin makiya yahudawan haramtacciyar kasar Isra’ila a kudancin Gaza.

“Ya kamata makiya su sani cewa shahadar kwamandoji, jarumai, da shugabanni ba zai raunana tsayin daka da al’ummar musulmi suke yi a gaban cin zarafi da zalunci da mamaya ta yahudawan sahyuniya ba,” inji Pezeshkian.

Sannan kuma ya yi ishara da wata Magana ta Ismail Haniyeh, tsohon shugaban Hamas da ya yi shahada inda yake cewa, “Idan wani shugaba ya fadi wani zaiya tashi.”

Sinwar ya yi gwagwarmaya da turjiya da jarumtaka har zuwa numfashinsa na karshe, bai nuna gajiwa ko mika wuya ba ,” in ji shugaba Pezeshkian.

Shugaban na Iran ya kara da cewa shahadar jagoran Hamas abu ne mai zafi da sanya damuwa ga daukacin al’ummar duniya masu neman ‘yanci musamman ga al’ummar Palastinu, amma kuma hakan wata alama ce dake kara tabbatar da gaskiya da sahihancin tafarkin da suke gwagwarmaya a kansa da makiya Allah, yahudawan sahyuniya masu aikata laifuka yaki da kisan bil adama da zubar da jinin kanan yara a bayan kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments