Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar.
“Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba.
Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar da kin amincewar da Iran ta dade tana yi na yin watsi da shirye-shiryen mallakar makamin nukiliya, wanda kasashen yammacin duniya ke zarginta da neman bama-baman nukiliya.
“Muna shirye don yin shawarwari, ba kai tsaye ba. Ba mu amince da su ba. Dole ne a yi tattaunawa bisa mutunta juna inji shugaban kasar ta Iran.
“Ba mu taba kera bama-bamai na nukiliyaba, ko a baya, a yanzu, kuma ba ma nan gaba ba.
“Ba za mu nemi yaki ba, amma za mu tsaya tsayin daka kan duk wani zalunci.
“Muna son zaman lafiya, musamman ma a kasashen musulmi da makwabtanmu.