Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci takunkumin maimakon mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin malla.
“Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, domin hakan ya yi hannun riga da maslahar Iran.
Amurka da kawayenta, wadanda ake kira da E3, sun ki amincewa da wani daftarin kuduri daga Rasha da China, wanda ya nemi jinkirta aiwatar da tsarin dawo da takunkumai kan Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA.
Pezeshkian ya kara da cewa Amurkawa “suna son mu ba su dukkan sinadarin uranium da aka tace, wanda ba za a amince da shi ta kowace hanya ba.”
Shugaban na Iran ya nanata cewa da alama Amurka za ta matsa kaimi don “fara mayar da martani” na takunkumin a cikin watanni masu zuwa, yana mai kara jaddada cewa idan aka tilastawa Iran yin zabi, to za ta zabi abin da ya dace da maslaharta da al’ummarta, maimakon biyan bukatar da ta yi hannun riga da maslahar kasa, yana mai shan alwashin cewa “duk da haka, za mu magance dukkan matsalolinmu.”
Ya ba da tabbacin cewa, an dauki matakan da suka wajaba don wannan yanayin, yana mai nuni da kawancen Iran da kasashe makwabta, BRICS, da kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kuma juriyar al’ummar Iran, duka za su taimaka wajen shawo kan wannan lamarin.”