Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada matsayar Iran na kaucewa yake-yake da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai jaddada cewa kasarsa ta na da ‘yancin mayar da martani ga masu tsokana.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Vatican Cardinal. Pietro Parolin, shugaban kasar Iran, yayin da yake yabawa matsayin gwamnatin Vatican na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, domin kawo karshen laifukan da yahudawan sahyoniya ke aikatawa a zirin Gaza.
Bayan shafe watanni 10 ana yaki, kuma akasin duk wani abin da ake zato, ya cutura bisa la’akari da goyon bayan Amurka ke ba Isra’ila.
Shugaban na Iran ya kara da cewa, wasu kasashen yammacin duniya, da kungiyoyin kasa da kasa, sun karfafa mamaya da Isra’ila ke wa Falasdinu saboda shirun da su ke.
A nasa bangaren, Parolin ya mika sakon taya murna daga Paparoma Francis zuwa ga shugaba Pezeshkian kan zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasar Iran, sannan ya yaba da matsayin sabon shugaban na Iran kan kyakkyawar hulda da kasashen duniya da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Dangane da halin da ake ciki a Falastinu, Parolin ya jaddada bukatar gaggauta kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa fararen hula a Gaza da kuma gaggauta tsagaita bude wuta a wannan yanki.