Pezeshkian: Dakatar Da Hare-haren Isra’ila Shi Ne Abu Mafi Mahimmanci A Gare Mu  

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce babban abin da ya kamata kasashen yammacin Asiya su sanya a gaba shi ne dakatar da hare-haren da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce babban abin da ya kamata kasashen yammacin Asiya su sanya a gaba shi ne dakatar da hare-haren da Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon da kuma Syria.

“A yau, mun taru a yanayi mai sarkakiya, da rashin kwanciyar hankali,” in ji shi a wani taro kan halin da ake ciki a zirin Gaza a gefen taron D-8, da ya gudana a wannan Alhamis a birnin Alkahira na kasar Masar.

“Yayin da muke gab da kammala kwanaki na karshe na watan goma sha hudu na yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza, muna ganin munanan ayyukan ta’addanci da laifuffukan da aka aikata kan al’ummar Palasdinu, haka kuma a ‘yan watannin baya-bayan nan, gwamnatin sahyoniya tana kai hare-hare na rashin Imani kan Lebanon da Syria,” inji shi.

Har ila yau shugaban na Iran ya jaddada cewa ba za a bata lokaci ba wajen tunkarar irin wadannan laifuffuka da ayyukan wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa dole ne a ba da fifiko ga hadin kai domin taka wa Isra’ilar birki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments