Rahotanni daga Ramallah sun ce a kalla sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila 3 ne su ka jikkata sanadiyyar taka su da mota da wani Bapalasdine ya yi , a yau Talata.
Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ambaci cewa; Wani Bafalasdine ya soka wa dan shayoniya wuka da aka dauke shi zuwa asibiti domin karbar magani.”
Majiyar ta ce da akwai sojojin a wurin da aka kai hari, don haka su ka bude wuta akan maharin Bapalasdine.”
Su kuwa jaridun Falasdinawa a Ramallah sun ce wanda ya kai harin na Yau Talata ya yi shahada bayan da sojojin mamaya su ka bude masa wuta.
A gefe daya, kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinawa sun yi maraba da harin akan ‘yan sahayoniya a kusa da Ramallah, tare da bayyana shi a matsayin mayar da martani ga laifukan yakin da suke tafkawa akan al’ummar Falasdinu.
Kungiyar Hamas da ta fitar da bayani ta yi jinjina akan ci gaban gwagwarmaya a yammacin kogin Jordan, duk da matsin lamba da takurawar da sojojin mamaya suke yi.
Haka kuma ta ce; jinanen shahidai za su ci gaba da zama masu karfafa gwiwar mutane domin ci gaba da yin gwgawarmaya.
Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta bayyana harin da cewa, Na jarunta ne’ kuma mayar da martani ne akan laifukan ‘yan mamaya.