Oman: Ba Iran Ce Ke Da Alhakin Fara Yaki Ba

Badr Bin Hamad Al-Busaidi ya bayyana hakan ne a shafinsa an X, inda ya yi ishara da banmbacin ra’ayi dangane da Iran da kuma abin
Ministan harkokin waken kasar Oman Badr Bin Hamad Al-Busaidi ya bayyana cewa, ba Iran ce ke da alhakin fara yakin da ake da shi a halin yanzu a yankin gabas ta tsakiya ba.

Ministan harkokin waken kasar Oman Badr Bin Hamad Al-Busaidi ya bayyana cewa, ba Iran ce ke da alhakin fara yakin da ake da shi a halin yanzu a yankin gabas ta tsakiya ba.


Badr Bin Hamad Al-Busaidi ya bayyana hakan ne a shafinsa an X, inda ya yi ishara da banmbacin ra’ayi dangane da Iran da kuma abin da yake faruwa a tsakanin kasashen yankin.


Ya ce dole ne a yi adalci a kan wanann batu, duk yadda ake da sabanin mahanga amma kuma dole ne a yarda cewa ba Iran ce ke da laifin fara yaki ba, an kawo mata hari ne babu gaira babu sabar.


Ya ci gaba da cewa, rufe mashigar Hormuz lamari ne wanda ya cutar da kowa a duniya, amma kuma dole ne a koma a kan dalilin da musabbabin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted