Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani kan batun a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X.
Ya karbi sakon ne daga hannun takwaransa na Oman Badr Albusaidi, wanda ya gudanar da wata gajeriyar ziyara a Tehran.
Saidai ministan harkokin wajen Iran din bai bayyana abinda shawarwarin ke kunshe da ba, amma ya jaddada cewa za a duba su a kuma mayar da amsa wacce ta yi daidai da muradin kasar da kuma hakkokin al’ummar Iran.
Har ila yau, a ranar Asabar, Araghchi ya sake jaddada ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na inganta sinadarin Uranium don zaman lafiya, yana mai cewa hakki ne na kasa da ba za a iya tattaunawa a kai ba.
Tun a watan Afrilu ne dai Iran da Amurka suka faro tattaunawa a shiga tsakanin kasar Oman a kokarin warware sabanin dake tsakanin bangarorin biyu dama wasu kasashen yammacin duniya kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya.
Kasashen dai na zargin Iran da kokarin mallakar makamman kare dangi batun da Iran ke musantawa tana mai cewa shirinta na lumana ne.
Amurka dai na son Iran ta rage inganta sinadarin uranium din ta zuwa “sifili.” Abinda iran ke cewa ba zai yi wu ba.