Nukiliya : Tehran ta soki rahoton IAEA da cewa bai da tushe

Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da

Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da tuhume-tuhume mara tushe kan shirin nukiliyar kasar.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tehran za ta mayar da martani ga duk wani matakin da bai dace ba daga kasashen Turai da Amurka.

Faransa, Jamus da kuma Ingila, tare da goyon bayan Washington, suna son yin amfani da wannan rahoto don aiwatar da wani tsari da zai ba da damar maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran.

A cikin rahoton nasa, Rafael Grossi ya bayyana cewa Iran ta inganta shirinta na inganta makamashin Uranium sosai, wanda ya hada da ingantawa zuwa kashi 60%, matakin da ya kai kusan kashi 90% da ake amfani da shi wajen kera makaman nukiliya.

Ya kuma zargi Tehran da rashin bayar da cikakken hadin kai ga hukumar.

Ya kuma ce “Iran ita ce kasa daya tilo da ba ta da makaman nukiliya da ke inganta uranium a wannan matakin.

Wannan rahoton dai na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da taro na gaba na hukumar gudanarwar IAEA a ranar Litinin mai zuwa 8 ga watan Yuni a Vienna, inda za a tattauna batun nukiliyar Iran.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha nanata cewa inganta sinadarin Uranium zuwa kashi 60 cikin 100 na cikin tsarin da take da shi na kare hakkinta na nukiliya cikin lumana, msuamman a fannin masana’antu da kiwon lafiya.

Iran ta sha bayyana cewa tana bada hadin kai ga hukumar ta IAEA, amma kasar ta sha yin gargadi akan yadda hukumar ta IAEA ke amfani da siyasa da kuma zama ‘yar amshin shatan wasu kasashen yammacin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments