An cimma matsaya ta karfafa bangaren sufuri da nufin inganta tattalin arzikin kasa a hukumance, a zaman taron majalisar ministoci na wannan mako da aka yi a jamhuriyar Nijar
Tun bayan cimma yarjejeniyoyi da kasashe aminan Nijar ne shugaban majalisar soji Janar Abdurahaman Tiani ya bayyana bukatar ganin an aiwatar da sauye-sauye a fanoni da dama a wannan kasa.
Fanoni da suka hada da sufuri,noma,tattalin arziki da tsaro,samar da wannan kamfanin sufurin jiragen kasa na Nijar (SNTR) wani bangare ne na aiwatar da dabaru na ci gaban sashen sufurin Jiragen kasa a cikin yankin Sahel da yammacin Afirka (AES).
Wasu daga cikin masu kula da sashen sufuri,sun bayyana tasirin wannan mataki wanda zai kuma shafi bangarori da dama,