Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani

Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar

Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni.

Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace mulki a shekarar 2023, da kuma kamfanin Orano, mallakin kasar Faransa wacce ke da kashi 90% a arzikin urinum da ake fitawar shekarun baya.

A wani rahoto da gidan talabijin din kasar ta Nijar ya watsa da yammacin ranar Lahadi, an ambato shugaban kasar, Janar Abdourahamane Tiani, na tabbatar da “hakkin kasar na baje hajarta da albarkatunta da kuma sayar da su ga duk wanda ke son siyan su, bisa ga ka’idodin kasuwanci, cikin cikakken ‘yancin kai.”

Tun lokacin da sojoji suka kwace mulki a juyin mulkin 2023, Nijar ta juya baya ga faransa wacce ta yi mata mulkin mallaka, tana mai zarginta da tallafawa kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments