Nijar: Taron Kasa Ya Bukaci Sojoji Su Yi Mulkin Rikon Kwarya na Shekara 5

Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar. Haka zalika taron ya nemi a yi

Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar.

Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP, damar tsayawa takara a zabubuka masu zuwa, sannan a amince da islama a matsayin addini mai rinjaye a kasar.

Taron ya kuma bukaci rushe dukkan jam’iyun siyaya 172 a kasar.

A yayin rufe taron janar Tiani ya yi alkawarin biyan bukatun mahalarta taron.

A shekarar 2023 ne sojoji suka kwace mulkin Nijar, bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, bisa hujjar tabarɓarewar matsalar tsaro da rashin shugabanci na gari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments