Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyar maka hamshakin kamfanin nan na hakar uranium na faransa (Orano) a gaban kotu bayan gano sinadarai masu guba a yankin Madaoulela, dake arewacin kasar.
Dama dai Nijar da Orano sun sun shafe watanni suna takaddama kan sinadarin uranium da ake fitwarwa a kamfanin Somaïr, wanda aka mayar da shi mallakin kasar ta Nijar a watan Yuni.
Ministan Shari’a na Nijar, Alio Daouda, ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata nan.
Ministan ya ce an gano “ganguna 400 da ke dauke da samfuran sinadarai masu guba” a wani tsohon wurin hakar ma’adinan uranium a wani waje da Orano ya fice a yankin Arlit, wanda ke arewacin Nijar.
“Wannan kamfani ya cutar kuma yana ci gaba da cutar da lafiyar al’ummar Nijar ta hanyar amfani da sinadarai masu guba, da sanya rayuwar wasu cikin hadari, da kuma lalata muhalli.
Kamfanin ya ma ki bin umarnin kotu da kotunanmu suka bayar wanda ya tilasta masa na kwashe milyoyin tan na sharar tiriri mai guba na rediyoaktif da aka bari a sararin samaniya, in ji ministan na Nijar.
Ministan Shari’a na Nijar ya bayyana cewa Nijar ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don gurfanar da Orano da kuma samun diyya kan duk barnar da aka yi wa Nijar.”
Orano, kamfani ne mallakar gwamnatin Faransa, wanda ya maye gurbin Areva, wacce ke rike da ikon mallakar hakar uranium na Nijar sama da rabin karni, saidai bayan juyin mulkin sojiji a ranar 26 ga Yuli, 2023, sabbin hukumomin Nijar sun yanke dukkan yarjejeniyoyi tsakanin Nijar da Faransa, ciki har da na hakkin hakar uranium na Orano.