Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta haramta fitar da man fetur da na Diezel zuwa kasashen ketare a kokarin da ta ke yi na ganin ta magance matsalar karancinsa a cikin gida.
A wata takarda da ministan kasuwancin kasar ,Abdoulaye Seydou ,ya sanya wa hannun a ranar 12 ga wannan watan, gwamnati ta ce an dauki matakin ne domin biyan bukatunta na cikin gida.
Sanarwar ta kara da cewa, idan aka samu wadatuwar makamashin man fetur a cikin gida gwamnatin na iya sahalewa kamfanin dillancin man na Sonidep da matatar Soraz damar fitar da man zuwa kasashen wajen.
Gwamnatin ta umurci jami’an tsaron da shugabanin hukumar Custums da kuma jami’an ma’aikatar kasuwanci ta kasa da su tabbatar an bi umurnin sau da kafa tare da hukunta wadanda aka samu da laifin sabawa dokar.