Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran.
Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin.
Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen.
Nijar dai ta raba gari da faransa da ta yi mata mulkin mallaka, ta kuma kori kungiyoyin kasa da kasa da dama dake mata zagon kasa.
ta kuma rufe fidagen radiyoyi na kasashen yamma irinsu RFi da kuma BBC.
jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.