Gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya yi kira da a gaggauta sakin hambararen shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da matarsa Hadiza.
Tun a watan Yulin 2023 ne ake tsare da Bazoum a wani reshe na fadar shugaban kasar da ke Yamai, inda Likitansa ne kawai aka yarda ya ziyarce shi.
A cewar gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, Mohamed Bazoum da matarsa Hadiza ana tsare da su ba bisa ka’ida ba, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.
Su ma lauyoyin Mohamed Bazoum A cikin wata sanarwa, sun tunatar da cewa tsohon shugaban da matarsa ”an hana su mu’amala da kasashen waje” dangi, abokai da ma lauyoyi tun daga Oktoba 2023.
A watan Yunin da ya gabata ne Nijar ta cire kariyar Mohamed Bazoum na shugaban kasa, lamarin da ya share fagen yi masa shari’ar da har yanzu ba a sanya ranar da za a yi ta ba.
Lauyoyin Bazoum dai sun ce gwamnatin mulkin sojan kasar na amfani da shi a matsayin garkuwar dan Adam”