A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin.
Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari Bizo yana nuna jin dadinsa da komawar shugaban kasar sannan ya kara da cewa, batun gina kasa da hadin kan al’umma shi ne abinda suke son ganin ya tabbata.”
A tsawon lokacin da yake rangadin, shugaban kasar ta Nijar ya yi kira ga al’umma da su zama masu tsayin daka,su kuma sojoji su kasance masu zama cikin fadaka da sa ido.
Ana daukar wannan ziyarar ta shugaban kasar a fadin kasar a matsayin kokarin sake tabbatar da hadin kai a tsakanin al’ummar kasar.
Fiye da shekaru 10 kenan Jamhuriyar Nijar take fuskantar matsalolin ta’addanci.
Wani mai fafutukar, Dr.Iro Tanimou ya fada wa manema labaru cewa, ziyarar da shugaban kasar ya kai a fadin kasar, yana nuni ne da sadaukar da kansa,kuma abin alfahari ne yadda ya ziyarci wurare da suke akan iyakokin Burkina Faso da Aljeriya.