Kasashen NIjar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu a bangarori da dama.
Bangarorin sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a yayin ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin cikin gida da tsaron jama’a da wata tawagar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar tsaron kasa Birgediya Janar Ahmad Rezaei RADAN.
A yayin wannan zama Nijar da Iran sun amince da kafa kwamitin kwararru domin yin musayar ra’ayi lokaci-lokaci da karfafa hadin gwiwa.
Nijar da Iran, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a fagen yaki da ta’addanci, da manyan laifuffukan kasa da kasa, tsaron iyakoki, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba.