Nijar : An nada Janar Tiani, a mukamin shugaban rikon kwarya

A Jamhuriyar Nijar, an daga martabar Abdourahmane Tiani madugun juyin mulkin sojin kasar daga mukamin Birgediya Janar zuwa Janar, mukamin soji mafi girma a kasar.

A Jamhuriyar Nijar, an daga martabar Abdourahmane Tiani madugun juyin mulkin sojin kasar daga mukamin Birgediya Janar zuwa Janar, mukamin soji mafi girma a kasar.

An ba Abdourahmane Tiani wannan mukamin ne bayan tabbatar masa da mukamin shugaban rikon kwarya na kasar a bikin da aka gudanar a jiya Laraba a Yamai babban birrin kasar.

Kafin hakan kuma Janar Abdourahamane Tiani, ya sa hannu kan dokar tsarin mulki na wucin gadi, mai taken “Tsarin farfado da Nijar”.

Bisa wannan doka, Tiani zai jagoranci kasar tsawon shekaru 5 tun daga ranar kaddamar da dokar, yayin da ainihin wa’adinta zai danganta da halin tsaro, da bukatun farfadowar kasar, da kuma ajandar kawancen kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.

Hukumomin wucin gadin sun kunshi shugaban jamhuriyar Nijar, da kwamiti mai kula da harkokin tsaron kasar, da gwamnati da kwamitin sulhu, da hukumar sa ido kan harkar jin kai da sauransu. 

Wata dokar kuma da shugaban rikon kwaryar ya sanya wa hannu a jiya ita ce ta rusa dukkanin jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar.

An amince da wannan sabon tsarin mulki ne bisa kudurorin da aka tattara, a yayin taron farfado da kasa da aka gudanar a tsakanin ranakun 15 zuwa 19 ga watan da ya gabata a birnin Yamai, fadar mulkin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments