Rahotanni da suke fitowa daga Nijar sun bayyana cewa; Wata kungiyar mai alaka da al-ka’ida ta dauki alhakin kashe sojojin kasar 11 a kan iyaka da Aljeriya.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai lamarin ya faru,kuma a jiya Asabar ne aka yi jana’izarsu a garin Agadez, kamar yadda wata majiyar watsa labara ta jamhuriyar Nijar ta ambata.
Shafin “Air Info” da ya watsa laabrin ya kuma ce; Jami’an soja da dama sun hjalarci jana’izar sojojin da su ka kwanta dama, daga cikinsu har da janar Musa Salih Barmo, babban hafsan hafsoshin sojan kasar.
Tashar Radiyo din kasar ta Nijar ta ce, an yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke sintiri akan mahadar iyakaokin kasar, da Mali da kuma Burkina Faso.
Labarin Radiyon ya kuma ce, Janar Barmo ya nufi asibitin garin Agadez din domin yin dubiyar sojojin da su ka jikkata.”
A gefe daya wata kungiyar mai suna; “Nasratul-Islam Wal Muslimin” da reshe ne na alka’ida, ta dauki alhakin kai harin.
A lokuta da dama a baya sojojin na jamhuriyar Nijar sun sha fuskantar hare-hare irin wadannan, sai dai ba kasafai kungiyoyin da suke ikirarin jihadi suke daukar alhakin kai wa ba.
Saharar dake Arewacin Nijar tana da girma kuma tana kusa da kasar Libya da masu hada-hadar mutane da kuma ‘yan hijira suke bi suna ratsawa domin shiga cikin kasashen turai.
Kungiyar “Ikilid” wacce ba ta gwamnati ba da take sa ido akan duk wasu rikice-rikice da suke faruwa a duniya, ta ce daga 2023 zuwa yanzu an kashe mutane 2400 a cikin wannan kasa.