Nijar: An Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Agaji Da Dama

Ma’aikatar harkokin cikin gida a jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da ayyukan kungiyoyi da dama masu gudanar da ayyukan agaji na cikin gida da

Ma’aikatar harkokin cikin gida a jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da ayyukan kungiyoyi da dama masu gudanar da ayyukan agaji na cikin gida da kuma na kasa da kasa, saboda rashin fitar da bayanai akan yadda harkokin kudi.

Bayanin ma’aikatar harkokin cikin gidan bai tantance adadin kungiyoyin da aka dakatar da su ba, sai dai wasu majiyoyi sun ce sun kai daruruwa.

A karshen makon da ya shude ne dai aka fitar da sanarwar ta kafofin watsa labaru da su ka hada Radiyo  da ake Magana da gwamnonin jahohi akan matakin.

Bugu da kari bayanin ya ce; kungiyoyin da aka buga sunayensu a cikin jaridu ne kadai aka bai wa izinin ci gaba da gudanar da ayyyukansu, da adadinsu ya kai 140, daga ciki da akwai 65 na  waje sai kuma 75 na cikin gida.

Wasu bayanan gwamnati sun sanar da cewa,ya zuwa 2024 adadin kungiyoyin fararen hula na waje da aka yi wa rijista a kasar sun kai 300, sai kuma wasu dubu 3 na cikin gida.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments