Nigeria: Wani Bom Da Ya Tashi A Maiduguri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 7

Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar

Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri.

Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka.

Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam.

An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da zirga-zirgar ababen hawa zuwa Damboa,Chibok da kuma wasu kananan hukumomi da suke a kudancin Jahar.

Ana barin matafiya su bi ta hanyar ne sai biyu a mako daya, bayan sojoji sun yi sintiri da kuma tabbatar da cewa ba a dasa abubuwan fashewa ba. Kusan shekaru biyu kenan ana yin haka. Tuni dai aka dauki wadanda su ka jikkata da ba a tantance adadinsu ba zuwa asibitin cikin Maiduguri domin yi musu magani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments