NIDCOM: An Ceto ‘Yan NAjeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Kurkuku A Libya

Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Najeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar

Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Najeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025.

Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87, da jarirai 54.

An samu nasarar mayar da su ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin NIDCOM, Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da kuma Hukumar Kula da Baƙin Haure da waɗanda rikici ya raba da matsugunansu (NCRMI).

A cewar sanarwar da NIDCOM ta fitar, an dawo da su ne kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris 2025.

A ranar 28 ga Janairu, an dawo da mutum 152. A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320.

Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici.

Ta kuma jaddada cewa wajibi ne ‘yan Najeriya su bi hanyoyin da doka ta tanada idan suna son yin hijira, domin guje wa hatsarin da ke tattare da tafiya ta haramtacciyar hanya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments