Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai.
Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa, bai ji kamlar kisan kiyashi ba, a cikin abinda aka ambata.
Wannan bai hana Fira ministan na HKI sukar takwaransa na Canada ba,tare da bayyana shi a matsayin mai kin jinin yuhudawa.
Su kuwa kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin kasar Canada sun bayyana ja da bayan da Fira minstan ya yi da cewa, ba abinda za a laminta da shi ba ne, ya zama wajibi a gare shi da ya goyi bayan MDD da kungiyoyin kasa da kasa na kare hakkin bil’adama akan cewa; Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Alaka a tsakanin HKI da kuma kasar Canada suna kara kamari,a lokacin da kungiyoyin kasa da kasa suke kara yi wa Tel Aviv matsin lamba akan kawo karshen yakin da take yi a Gaza.