Nawwafa Salam: Yin Mu’amalar Diplomasiyya Da “Isra’ila” Ba Shi Alfanu

Shugaban gwamnatin kasar Lebanon Nawwaf Salam ya bayyana cewa: Tun da ya kafa gwamnati yake aiki da dukkanin hanyoyi domin yin matsin lamba akan HKI

Shugaban gwamnatin kasar Lebanon Nawwaf Salam ya bayyana cewa: Tun da ya kafa gwamnati yake aiki da dukkanin hanyoyi domin yin matsin lamba akan HKI ta daina keta hurumin kasar, sannan kuma ta janye daga wuraren da ta shiga, tare da sakin fursunonin da take rike da su.”

Nawwaf Salami ya kara da cewa; Bude kafar diplomasiyya da aiki da ita a wannan fage, bai bayar da wani sakamako ba, watakila kuma zai dauki lokaci mai tsawo a nan gaba.”

Shugaban gwamnatin kasar ta Lebanon ya kuma ce; A yanzu muna cikin halin yaki ne da “Isra’ila”, wani lokaci ya yi tsanani, wani lokacin kuma ya yi sauki,illa iyaka muna kokarin ganin an kawo karshen hakan.”

Dangane da batun bude tattaunawa da HKI ta hanyar shiga tsakani, shugaban gwamnatin kasar ta Lebanon ya ce; Hakan ba ya cikin abinda ke gabanmu, har sai illa masha Allahu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted